Kakakin Majalisar Dokokin kasar Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko- farkon samun nasarar juyin juya halin Musulunci wata jarrabawa ce wacce Iraniyawa suka shiga don kare kansu irin halin da suka tsinci kansu a yanzu.
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a Majalisar Dokokin Iran, ya kuma kara da cewa: Ranar 22 ga watan Satumban shekara ta 1980, rana ce wacce Saddam Hussain na kasar Iraki ya farma kasar Iran da yaki da nufin durkusar da ita tun tana jaririya, amma sai da aka fafata tsawon shekaru 8 bai sami nasara ba.
Wannan yakin shekaru 8, shi ne ya mai Iraniyawa mayaka masu sa kai zuwa runduna mai karfi wacce a yau take neman hakkin al’ummarsu daga hannun daya daga cikin manyan kasashe masu girman kai a duniya.
Ya ce yakin shekaru 8 ne ya mai da Iran abin da take yau, inda take fafatawa da kasa mafi girma a duniya a fagen makamai da kuma karfin tattalin arziki, kuma da yardan Allah ta samu nasara a kansu.