Babban magataardar kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Lebanon, Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Gwgawarmaya ce kadai hanyar ‘yantar da kasa da kuma fuskantar “Isra’ila”.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma kara da cewa; Babu wata hanya da za a iya fuskantar Isra’ila da girman kai na duniya, idan ba ta hanyar gwgawarmaya ba.
A wani jawabi da ya yi dangane da taron karawa juna sani domin cika shekaru 55 da kafa kungiyar daliban mazhabar Imamiyyah ta Pakistan, sheikh Kassim ya kuma ce; A kasar Lebanon mun jarraba gwgawarmaya mun kuwa fahimci cewa ta hanyarta ne ake iya ‘yantar da kasa da mutum da kuma korar abokan gaba-Isra’ila a cikin kaskanci, sannan kuma ta sake dawo da batun falasdinu a matsayin batu mafi muhimmanci.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Abinda gwagwarmaya take nufi shi ne kin amincewa da makiya da kuma yakarsu idan an sami dakar yakin ta hanyoyi daban-daban.
Da yake Magana akan yakin wuce gona da iri na Amurka da Isra’ila akan Iran, Sheikh Na’im Kassim ya ce; Iran ta yi nasara,domin manufar yakin ita ce kawar da tsarin musulunci, to amma su ka fuskanci kalubale.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma yi kira ga matasa da su ci gaba da aiki da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi da kuma gwagwarmaya.