Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’ila baqai ya soki kasar Amurka game da kokarinta na ficewa daga yarjejeniyar Islamabad da aka cimma tsakaninta da kasar iran a watan yuni da gangan,
kakakin yayi wannan bayanan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin din kasa a jiya Asabar game da batun yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin iran da Amurka da Pakistan ta jagoranta, domin kawo karshen yakin da Amurka da isra’ila suka fara shi kan kasar iran, daga ranar 28 ga watan fabareru zuwa 7 ga watan Aprilu
Kasar Amurka ta juyawa yarjejeiyar baya ne bayan ta zargi dakarun sojin kasar iran da kai hari kan jiragen ruwanta guda 3, sai dai Baqa’I yayi watsi da zargin , yace babu wasu cikakkun bayanai ko hujjoji ingantatu dake tabbatar da afkuwar hakan.
haka zalika yace Washington na shirya wata makarkashiya da za ta yi amfani da ita wajen ficewa daga yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma matsaya akai, da bata kare maslaharsu ba, kuma ya jaddada cewa idan ma akaddar batun karya yarjejeniyar ya faru to tattaunawar ta samar da tsarin da zaa bi wajen warware sabani da aka samu.