Shugaban kwamitin tsaro a Majalisar Dokokin Kasar Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa: Akwai yiyuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fice daga yarjejeniyar NPT ta hana kera makaman nukiliya tare da hana yaduwarta a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Ibrahim Azizi yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma yi kira ga kasashen larabawa na yankin Tekun Farisa su hada kai da Iran mai karfi don kawo ci gaban wannan yankin.
Ya ce a halin yanzu, yakin da Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka dora wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sauya yankin Gabas ta Tsakiya har abada, kuma zai sauya hatta yadda duniiya take nan gaba. Azizi ya ce an dade Hukumar Kula da Makamashin Nukliya ta Duniya IAEA tana aiki wa mikiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tana kuma cutar da ita. Suna ganin lokaci yayi da zasu kawo karshen hulda da wannan Hukumar tun da ba aiki take yi domin ci gaban kasashe ba.