Iran Ta Gabatar Da Sharudda 7 Na Tsayar Da Yaki Da Amurka

Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran Janar Mohsen Riza’i ya bayyana cewa: Idan Amurka tana son kawo karshen yaki da Iran, to dole ne

Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran Janar Mohsen Riza’i ya bayyana cewa: Idan Amurka tana son kawo karshen yaki da Iran, to dole ne ta amince da wadannan sharudda, daga cikinsu akwai dakatar da yaki a dukkan fagagen fama, sakin dukkan kudaden Iran da aka tsare da kuma kawo karshen killacewar da sojojin Amurka suka yi tasoshin jiragen ruwa na kasar.

Labarin ya kara da cewa: A wannan karon Iran bata son a sake far mata da yaki, saboda haka ta bukaci dukkan sojojin Amurka su fice daga yankin yammacin Asiya.

Kafin haka dai, Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun farwa Iran da yaki na tsawon kwanaki 12 a cikin watan Yunin shekara ta 2025. Sannan suka sake farma kasar da yaki a ranar 28 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

A cikin yakin, sun yi sanadiyyar shahadan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Ali Khamene’i, sannan suka kai hare hare kan cibiyoyin makamashin Nukiliyar kasar a Isfahan, Natanz da kuma Fardo, banda dubban mutane da suka kashe wadanda suka hada da janarorin sojojin kasar da manya -manyan Jami’an gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted