Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Janar Muhsin Rizha’i ya wallafa sako a shafinsa na sada-zumunta cewa; Amurka ba ta da wata mafita da ya wuce ta yarda da hakkokin al’ummar Iran da kuma karbarsu.
Haka nan kuma ya ce, fara kowace irin tattaunawa da Amurka yana da alaka ne da karbar sharudda 7 na Iran, kuma abubuwa ne da suke a fili.
Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran din ya kuma ce; Lissafin da shugaban kasar Amurka ya yi akan Iran kuskure ne,kuma a halin yanzu Iran tana cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci domin kare kanta idan har aka kawo mata hari. Har ila yau ya ce, Iran din za ta kai wa sansanonin Amurka hare-hare da kuma manufofinta a cikin wannan yankin fiye da kowane lokaci.
Janar Rizha’i ya kuma ce; Iran tana tattaunawa da Qatar a kodayaushe wacce ita kuma take aikewa da sako zuwa ga Amurka. Daga cikin sharuddan Iran da akwai kawo karshen dukkanin yake-yake a cikin wannan yankin, da kuma mayarwa da Iran kudadenta da ake rike da su, sannan kuma da kawo karshen killace ta da aka yi.
Akan Shirin Iran na fasahar makamashin Nukiliya, Muhsin Rizha’i ya kuma ce; Har yanzu Iran tana kan fatawar jagora shahidi, kuma babu abinda ya sauya, sai dai kuma duk da haka babu tabbaci akan abinda zai faru a nan gaba.