Hizbullah:Gwagwarmaya Ce Hanya Daya Wajen Yanto Falasdinu

kungiyar hizbullah ta kasar labanon ta ce gwagwarmaya ce hanya daya tilo ta yanto kasa da yanci

Babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon shaikh Naim Qaseem ya jaddada cewa kalubalantar isra’ila da masu girman kai na duniya ba zai yi yu ba sai ta hanyar gwagwarmaya, kuma ya jadda game da muhimmanci lamarin falasdinu , da kuma nasarar da kasar iran ta samu a yakin da tayi da makiya sakamakon tsayin daka ta yi.

A cikin wani jawabi da yayi a wajen taron da aka yi kan shahidi dan gwagwarmaya na cika shekaru 55 da kafa kungiyar dalibai yan imamiya a kasar Pakistan shaikh Qasem yace gwagwarmaya ce hanya daya tilo wajen kwatar yanci.

Yace mun gwada a kasar labanon mun gani cewa lallai gwagwarmaya tana kwatar kasa da dan adamtaka, kuma ta kori israila da karfin tsiya cikin kaskanci kamar yadda ta take bawa batun falasdinu matsayi da ci gaba da wanzu

Daga karshe da yayi ishara game da harin da amurka da isra’ila suka kai wa iran, yace” manufar kai wa iran hari shi ne yunkurin kifar da gwamnati sai dai bayi nasara ba saboda gwagwarmaya,  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted