Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-OJO ya ce Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti mai zaman kansa dake da mambobi 10 domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar wasu matasa 37 sakamakon kullesu a wani dakin ajiye masu laifi na hukumar Civil Defence ta yi.
An gano gawarwakin matasan 37 ne a cikin wani dakin ajiye masu laifin a Minna, babban birnin jihar Niger, ranar Alhamis bayan kama su bisa zargin hakar zinare ba bisa ka’ida ba, a wani samame da jami’an hukumar tsaro ta farar hula ta Najeriya wato Civil Defence (NSCDC) suka yi.
Wadanda suka tsira sun ba da labarin cewa an cunkusasu a cikin wani daki karami wadda babu lafiyayyar iska a ciki, sannan daya daga cikinsu ya ce an fesa musu wani abu da ya toshe musu makogwaro da hancinsu a cikin dakin kafin a rufe kofar.
Shugaba najeriya Bola Tinubu a ranar Juma’a ya ba da umarnin gudanar da sahihin bincike cikin gaggawa, a game da musabbabin mutuwar wadannan matasa. Tinubu Ya ce ba zai lamunci wannan danyen aiki da aka yishi na cin zarafi da rashin mutunta rayuwar matasan ba.