Kasar Iran Ta Bayyana Sharudda 7 Ga Amurka Idan Tana Son

iran ta shinfidawa amurka sharudda 7 idan tana so na fice daga cikin mawuyacin yanayi

Babban sakataren kolin tsaron kasa major janaral Mohsen Rezaei ya bayyana sharuddan kasar iran guda 7 idan amurka na son a ci gaba da tattaunawa tsakani,  yace dole Washington ta amince da sharuddan iran idan tana son kubuta daga matsalar da haifar  sakamakon harin da ta kaddamar kan kasar iran

Babban jam’in tsaron kuma mai bawa jagoran juyin musulunci na kasar iran shawara kan harkokin tsaro yayi wannan bayanin ne a shafinsa na X a jiya Asabar adaidai lokacin da ake fuskantar jinkiri a tattaunawar da ake yi tsakanin iran da Amurka domin kawo karshen yakin, sakamakon ayyukan barna da amurke ke tafkawa a yankin

Kasar iran ta shimfidawa Amurka sharuddanta idan tana so a fara wata tattaunawa, sakon Tehran a fili yake kuma bazaa canza ba, idan Washington tana son ta fitar da kanta daga cikin mawuyacin halin da ta haifar , kuma ta guji  kara shiga cikin rikici, ba ta da wani zabi sai dai  ta amince da hakokin iran da Kaidojinta

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted