Sojojin Isra’ila Sun Kama Falasdinawa 100 Daga Sanda Aka Fara Azumin Watan Ramadana

rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kama falsdinawa guda 100 a fadin yankin gabar yammacin kogin jodan  daga lokacin da aka fara Azumin watan

rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kama falsdinawa guda 100 a fadin yankin gabar yammacin kogin jodan  daga lokacin da aka fara Azumin watan Ramadan zuwa yanzu kamar yadda kungiyar kare hakkokin falasdinawa fursunoni ta bayyana.

A cikin wani rahoto da suka wallafa ya nuna cewa kungiyar ta pps ta ce binciken ya fara ne tun a ranar laraba da ta gabata lokacin da aka fara Azumin watan Ramadan, inda sojojin Isra’ila suka fara shiga cikin garuruwa da sansanin yan gudun hijira a cikin dare suna kama falasdinawa.

mata da dama da yara kanana suna daga cikin wadanda aka kama , a jiya lahadi ma sojojin Isra’ila sun kama falasdinawa guda 8 da suka hada da yara guda 3 a lokacin da suka kai samame a garin qalqiliya dake kusa da garin Azzun.

haka zalika sojojin Isra’ila sun tsaurara tsaro a shingayen sojoji  tun daga farkon Ramadan . sama da shingayen soji na din din din dana wucin gadi guda 1000 ne suke takaita zirga zirgar ababen hawa da kuma tsannanta bincike a gabar yammacin kogin Jodan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted