Search
Close this search box.

 Sojojin HKI Suna Cigaba Da Yin Kisan Kiyashi A Gaza

Jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare a garin Rafah da kuma sansanin ‘yan hijira na Nusairat da Jabaliya, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar

Jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare a garin Rafah da kuma sansanin ‘yan hijira na Nusairat da Jabaliya, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar gwamman Falasdinawa da kuma jikkata wasu.

Rahotannin da suke fitowa daga yankunan da aka kai wa hare-haren sun ce; ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 14.

Dakunan adana kayan agaji dake sansanin ‘yan hijira na Jabaliya yana daga cikin wuraren da  sojojin HKI su ka kai wa harin, wanda kuma ya yi sanadin shahadar mutane biyu.

Wadannan hare-haren dai sun biyo bayan kutsen da sojojin mamayar su ka yi ne a cikin asibitin ‘Ash-shafa’ dake tsakiyar Gaza, tare da kashe babban jami’in yansanda sannan kuma da cinna wa dakin tiyata a cikinsa wuta.

Baya ga masu jiyya a cikin asibitin da akwai fiye da fararen hula 5000 da suka fake a cikinsa saboda kare rayukansu daga hare-haren da sjojin mamaya suke kai wa kowace kusurwa ta Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments