Dakarun Amurka za su kammala janyewa daga sansanin Air Base 101 da ke Nijar a ranar Lahadi 7 ga watan Yuli 2024, amma wasu dakaru da dama za su ci gaba da zama a sansanin sojin sama na biyu a kasar har zuwa watan Satumba, kamar yadda wani jami’in tsaron Amurka ya shaida wa Sputnik a ranar Juma’a.
Jami’in tsaron ya tabbatar da labarin janyewarsu daga sansanin sojin na Air Base 101 kusa da birnin Yamai zuwa ranar Lahadi.
Sai dai jami’in ya bayyana cewa yawancin sojojin Amurka 500 a halin yanzu a Nijar suna jibge a sansanin jirage marasa matuka na Air Base 201, kusa da birnin Agadez da ke arewacin kasar, inda ya kara da cewa sojojin za su ci gaba da zama a kasar har zuwa watan Satumba.
Ya ce “Za a kuma rufe sansanin Air Base 201, amma fifiko shine 101 da ke a Yamai a matakin farko, sannan Za a kammala janyewar AB 201 nan da 15 ga Satumba.” In ji shi.
Tun a watan Maris ne aka fara aiwatar da shirin janyewar sojojin na Amurka bayan da gwamnatin soji da ta karbi mulki a watan Yulin shekarar 2023, ta soke yarjejeniyar soji da Amurka nan take, saboda muradun al’ummar Nijar.
A cikin watan Mayun da ya gabata, bangarorin biyu sun sanar da cimma yarjejjeniyar raba gari da juna bayan shafe kwanaki da dama ana tattaunawa tsakanin tawagar ma’aikatar tsaron Amurka da takwarorinsu na Nijar a Yamai.
A wata hira ta musamman ga jaridar Washington Post, Fira Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya bayyana a watan Mayu cewa dangantaka da Amurka ta yi matukar tabarbarewa sakamakon yunkurin jami’an Amurka na yanke shawarar zabar wa Nijar kawancen kasashen waje da ya kamata ta yi daidai da mahangar Amurka, baya ga gaza samar da kwararan dalilai na kafa sansanin sojojin Amurka a kasar.