Search
Close this search box.

Sojojin Amurka Sun Kammala Ficewa Daga Sansaninsu Na Karshe A Nijar  

Sojojin Amurka sun kamala ficewa daga sansaninsu na karshe a Jamhuriyar Nijar. A jiya Litini ne akayi bikin ban kwana da ragowar sojojin da suka

Sojojin Amurka sun kamala ficewa daga sansaninsu na karshe a Jamhuriyar Nijar.

A jiya Litini ne akayi bikin ban kwana da ragowar sojojin da suka rage a sansanin mai lamba 201 dake birnin Agadas a arewacin Jamhuriyar Nijar.

Wannan na nufin babu wani sauran sojin Amurka ko kayayakin aikinsu da sukayi saura a yankin.

Kanal-Manjo Maman Sani Kiaou na hafsan soji na musamman, na Nijar da wakilin bangaren Amurka ne suka sanya hannu kan takardar kawo karshen janyewar, kamar yadda shafin jaridar Airinfo ya rawaito.

Bangarorin biyu sun bayyanawa manema labarai cewa ficewar sojojin ba wai yana nufin kawo karshen alakar soji dake a tsakanin kasashen ba.

Bangarorin sun kuduri aniyar ci gaba da tuntubar juna tare da yin aiki tare don fitar da sabon tsari na hadin gwiwar soja dangane da muradun kowane bangare da nufin karfafa tsaro da zaman lafiyar yankin,” inji sanarwar da bnagarorin suka fitar wacce jaridar Aïrinfo ta samu sami kwafinta.

A ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata ne aka fara aiwatar da yarjejeniyar janyewar sojojin na Amurka daga kasar.

Janyewar dakarun na Amurka daga kasar an yi shi cikin ruwan sanyi, sabanin na sojojin faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka.

Mazauna birnin Agadas sun jima da suke kokawa da kai kawo na jiragen sojojin na Amurka, musamman jiragenta marasa matuka wadanda ke rikitowa wasu lokuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments