Sojojin dake mulki a Guinea Bissau sun sanar da sakin wasu yan adawa guda 6, wadanda ake tsare da su tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata.
Mutane shidan da sojin Guinea-Bissau suka saki na da alaka da Domingos Simoes Pereira, jagoran jam’iyyar PAIGC wadda ta jagoranci kasar wajen samun yancin kai a shekarar ta 1974, kodayake ana ci gaba da tsare Pereira tun bayan juyin mulki.
Sakin yan adawar na bayyana dawowar turbar dimokradiyya da kuma mutunta dokokin kasa da kasa da gwamnatin sojin kasar ke yi.
Sojojin sun kwace mulkin ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, ana tsaka da shirye-shiryen sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar wanda shugaba Umaro Sissoco Embalo ya sake tsayawa takara.
A ranar lahadin da ta gabata ne, ministan harkokin wajen Senegal ya jagoranci wata tawaga zuwa Guinea-Bissau don wakiltar ECOWAS, bayan sojin dake mulki sun hana tawagar kungiyar sauka a cikin kasar.