Search
Close this search box.

Shugabar Kasar Tanzaniya Ta Mika Sakon Ta’aziyyarta Ga Gwamnatin Iran Da Al’ummarta

Kasar Tanzaniya ta mika sakon ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar Iran kan shahadar shugaba Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa Shugabar kasar Tanzaniya Samia Hassan ta

Kasar Tanzaniya ta mika sakon ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar Iran kan shahadar shugaba Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa

Shugabar kasar Tanzaniya Samia Hassan ta bayyana matukar jajenta da alhininta ga gwamnati da al’ummar Iran dangane da shahadar shugaba Sayyid Ibrahim Ra’isi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian, da abokansu bayan hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Kwana guda bayan sanar da shahadar Hujjatul-Islam Ibrahim Ra’isi da makarrabansa a hukumance, Samia Hassan ta aike da sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Iran tare da buga sakon a shafukanta na yanar gizo da na sada zumunta.

Ta kara da cewa: A madadinta da kuma a madadin gwamnati da al’ummar kasarta, tana bayyana bakin ciki da jin kai ga gwamnati da al’ummar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments