Bayanai daga Faransa na cewa mutane 7,184 aka kama tun bayan soma zanga zangar tsadar rayuwa a ranar 17 ga Oktoba 2026 a fadin kasar.
Daga cikin da akwai wasu 466 da aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari, a cewar alkaluman da Ministan Shari’a na kasar ya fitar ranar Talata.
Jerin kungiyoyi a faransa sun shiga zanga zangar tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi wacce ta samo asali daga fishin daliban makarantun sakandare dake zargin gwamnati da gazawa wajen warware matsalolin da suka dabaibaiye sha’anin ilimi a kasar.
Zanga zangar ta hada daliban makarantar sakandare, daliban jami’a, da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, bisa ga kiran kungiyoyin kwadago na gwamnati.