Shugaban Hamas Isma’il Haniyeh Ya Yi Shahada A Harin Isra’ila A Kasar Iran

Shugaban bangaren siyasar kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh ya yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta

Shugaban bangaren siyasar kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh ya yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar da shahadar Isma’il Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas na Falasdinu, da kuma mamba a tawagarsa ta masu ba da kariya gare shi a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau Laraba sun bayyana cewa: Isma’il Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da kuma mamba a tawagarsa ta kare shi a birnin Tehran sun yi shahada bayan an kai musu harin ta’addanci.

Kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Hamas na zaman makoki da mika ta’aziyya ga ‘ya’yan al’ummar Falastinu masu girma, da al’ummar Larabawa da na Musulmi, da kuma dukkanin ‘yantattun al’ummar duniya, kan shahadan dan gwagwarmaya Isma’il Haniyyah, shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas wanda ya yi shahada sakamakon wani hari na ha’inci da yahudawan sahayoniyya suka kai kan masaukinsa da ke birnin Tehran, bayan halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran Masoud Pezeshkian.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments