Amurka Tana Matsain Lamba Kan Kasashen Afrika Akan ICC

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donal Trump tana matsin lamba kan kasashen Afrika da su fice daga kotun duniya mai hukumta manyan laifuka, kuma tana yi

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donal Trump tana matsin lamba kan kasashen Afrika da su fice daga kotun duniya mai hukumta manyan laifuka, kuma tana yi musu barazanar fuskantar mummunan sakamakon idan suka ki yin hakan, adaidai lokacin da Washington take kara tsananta fadada take nuna adawa da wannan kotun

A cikin wani rahoto da jaridar le monde ta buga a jiya talata ta nuna cewa kasar Amurka tana amfani da hanyoyi biyu  wajen matsin lamba kan kasashen afrika don su fice daga kotun duniya ta ICC  ta hanyar yada bayanai na karya da nuna cewa gwamnatocin da aka kai wa hari za su iya fuskantar sharia

Hanya ta biyu kuma itace barazana ga kasashen da soke yarjejeniyar tsaron da suka kulla da Amurka da sauran ayyukan hadin guiwa  idan suka ki amincewa su fice daga kotun  kamar dai yadda rahoton ya bayyana.

kasar Uganda ta samu wasika daga kasar Amurka a ranar 24 ga watan yulin shekara ta 2026  inda aka bata wa’adi na ta fice daga kotun duniya ko kuma ta fuskanci mummunan mataki, duk da yake cewa har yanzu gwamnatin kampala bata mika wuya ga butakar ba, haka kuma Amurka ta fuskanci kasar Benin a wani bangare na matsin lamba, duk da cewa hukumimin kasar sun nuna kin amincewa da bukatar ficewa daga kotun ta ICC.

tun a ranar juma’a ne trump ya bukaci sakataren wajen Amurka Marco Rubios  ya fara kaddamar da yaki kan kotun ICC domin kare fira ministan HKi Benjamin Natanyaho, yace Ruboi yana kokarin kare Bibi  da sauran mutane ne a lokacin taron da aka gudanar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted