Shugaban Kungiyar Hamas A Gaza Ya Ce: Yahudawa Ke Hana Ci Gaba Da Tattaunawa

Babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Gaza ya bayyana cewa: Zaman tattaunawa kan batun Falasdinu ya lalace ne saboda rashin kiyayen sharudda daga

Babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Gaza ya bayyana cewa: Zaman tattaunawa kan batun Falasdinu ya lalace ne saboda rashin kiyayen sharudda daga ‘yan mamaya

Shugaban kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Zirin Gaza, Khalil al-Hayya, ya bayyana cewa: Harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan unguwar al-Daraj da ke Gaza, wanda ya yi sanadiyyar shahadar Hamza al-Sharbasi tare da raunata ɗansa Azzam, ci gaba ne na kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasɗinu kuma yana cikin matsin lamba na siyasa da yunƙurin tilasta bin munanan manufofin yahudawan sahayoniyya da ƙarfi.

Al-Hayya ya bayyana cewa: Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da tawagar Falasdinawa suke shirye-shiryen halattar zaman tattaunawa, yana mai nuni da abin da ya faru a birnin Doha na Qatar a ranar 9 ga watan Satumba na shekarar da ta gabata, idan aka yi la’akari da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila tana neman fitar da abin da take so ne ta hanyar aiwatar da kisan gilla da ta’addanci.

Khalil ya jaddada cewa: Shahadar Falasdinawa ko shugabanninsu ba za ta tsorata Falasɗinawa ba, yana mai jaddada cewa dukkan Falasɗinawa daidai suke a cikin sadaukarwarsu kuma “dukkanin al’ummar Falasɗinawa ana kai musu hari, ko kai tsaye ko a kaikaice.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted