Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye faye ya kaddamar da sabuwar jam’iyyarsa ta siyasa a jiya Asabr.
Wannan matakin dai ya biyo bayan sabanin da ya kunno kai ne a tsakaninsa da tsohon Fira Minista Usmanu Sanko a karkashin jam’iyyarsu ta “Pastef”.
Wannan sabanin ne ya sa shugaban kasar ya sauke Sonko daga kan mukaminsa na Fira minista, sai dai kuma majalisar dokokin kasar ta zabi Sonko a matsayin shugabanta.
Sabani na gaba da ya kunno a tsakanin bangarorin biyu shi ne yadda majalisar dokokin kasar ta fitar da wani kuduri da ya rage karfin ofishin shugaban kasa da kuma sauye cewa daga yanzu shugaban kasa ba zai ci gaba da zama shugaban jam’iyyarsa ba.
Ita kuwa kotun tsarin mulkin kasar wacce ita ce ta koli, da ta karbi karar da shugaban kasa ya gabatar, ta yi watsi da matakin majalisar tare da bayyana shi da cewa yana cin karo da tsarin Mulki.