Kakakin Tsaron IRGC Ya Bayyana Hasarar Da Suka Yi Wa Amurka Cikin ‘Yan Kwanakin Nan

Kakakin rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Sun lalata jiragen yaki da na helikopta na Amurka guda 11 da kuma jiragen sama

Kakakin rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Sun lalata jiragen yaki da na helikopta na Amurka guda 11 da kuma jiragen sama marasa matuka guda 17 a yayin yakin da ya dauki tsawon kwanaki 15

Brigadier Janar Hussein Mohebbi, kakakin rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta Iran ya sanar da cewa: Sojojin Iran sun lalata jiragen yaki da na helikopta na Amurka guda 11, tare da jiragen sama marasa matuka ciki guda 17, a sansanonin da ke yankin a yayin yakin da ya dauki tsawon kwanaki 15.

Brigadier Janar Mohebbi ya rubuta a shafin X cewa: “Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun lalata jiragen yaki da na helikopta na Amurka guda 11 a sansanonin da ke yankin -ciki har da samfuran F-15, P-8, C-17, da jiragen sama guda takwas masu samar da man fetur ga wasu jiragen sama a sararin samaniya—tare da jiragen sama guda 17 na leken asiri da na ayyukan soja.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted