Aragchi Ya Zanta Da Jami’a Mai kula Da Al-Amuran Harkokin Waje Na Tarayyar turai EU

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da jami’a mai kula da al-amuran harkokin wajen na tarayyar Turai EU Kaya Kalas ta wayar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da jami’a mai kula da al-amuran harkokin wajen na tarayyar Turai EU Kaya Kalas ta wayar tarho inda bangarorin biyu suka tattauna kan abubuwan da suke faruwa a yankin yammacin Asia da kuma a fagen kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran , ya nakalto Aragchi yana fadawa Jami’an na tarayyar Turai kan bukatar MDD da tarayyar Turai da kuma sauran kasashen duniya su yi tir da hare haren da kasar Ukraine ta kaiwa wani jirgin ruwan kasar Iran a tekun Caspian.

Aragchi ya bukaci kwamitin tsaro na MDD ya dauki mataki kan hare haren na Ukrain kan jirgin ruwan kasar Iran. Sannan ya bukaci kwamitin ya kira gwamnatin kasar Ukraine don amsa tambayoyi kan hakan.

Dangane da yakin da Amurka ta fara a yankin yammacin Asia jami’an guda biyu sun tattauna yanda yakin yake tafiya musamman marda martan JMI kan sansanonin sojojin Amurka a yankin.

Sun kuma bukaci bangarorin biyu su nemi hanyar tsaida yakin da kuma tare da neman hanyar tattaunawa don kawo karshensa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted