Muhammad Sharqawi wanda malami ne a jami’ar Goerge Mason ya ce;Amruka ta ki yarda da cewa Iran ta zama kasa mai karfi.
Malamin na jami’ar Goerge Mason ya kara da cewa; A tsakanin dukkanin sugabannin Amurka Barrack Obama ne kadai ya yarda da cewa, lallai Iran kasa ce mai karfi, don haka ya yi yarjejeniya da ita.
Sharqawi ya kuma ce; Shugaban Amurka na yanzu Donald Trump ne ya yi watsi da dukkanin sakamon da nazarce-nazarce da bincike su ka tabbatar akan karfin Iran, ya shelanta yaki akanta.