Ganawar Ministocin Iran Da China A Kyrgyzstan

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tabbatar wa takwaransa na China kudurin Iran na kare ‘yancinta da kuma mutuncin yankinta daga hare-haren ta’addanci Ministan harkokin wajen

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tabbatar wa takwaransa na China kudurin Iran na kare ‘yancinta da kuma mutuncin yankinta daga hare-haren ta’addanci

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi wanda ya ziyarci kasar Kyargyzistan domin halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), ya gana da takwaransa na kasar China Wang Yi.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna muhimman dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da ci gaban shiyyar da kasa da kasa, da batutuwan da suka shafi ajandar kungiyar SCO.

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da China sun jaddada dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China, inda suka jaddada aniyar shugabannin kasashen biyu wajen karfafa hadin gwiwa a fannonin moriyar juna da aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted