Gobara Tana Ci Gaba Da Lakume Dajuka A Kasashen Duniya Masu Yawa

A kasar Spain dake nahiyar turai mahukuntan kasar sun shelanta halin-ko-ta-kwana tun a jiya Asabar bayan da gobarar da kufce daga hannun masu kashe ta.
Wutar Daji A Cikin Kasashe Masu Yawa

Tsananin zafin da ake fama da shi a duniya ya yi sanadiyyar tashin gobara a cikin kasashe da yawa a nahiyoyi hudu.

A kasar Spain dake nahiyar turai mahukuntan kasar sun shelanta halin-ko-ta-kwana tun a jiya Asabar bayan da gobarar da kufce daga hannun masu kashe ta. Mafi yawancin gobarar ta kasar Spain tana tashi ne a kusa da babban birnin kasar Madrid, wacce aka bayyana da cewa; Ita ce mafi muni a tsawon tarihin wannan kasar.”

Haka nan kuma ana fama da wata gobarar a yankin Valancia a gabashin kasar ta Spain.

A tsakiyar kasar an dauke mutane 70,000 zuwa nesa da yankin da gobarar ta tashi, saboda su rayu cikin aminci.

A kasar Faransa wacce tsananin zafi ya addabe ta,an dauke mutanen da sun kai 300,000 daga yankunan da suke kusa da dajuka a yammacin kasar a kusa da garin Burdor, tare da cewa ba a taba ganin gobara irinta ba a tarihin kasar.

A kasar Moroko ma dai an sami gobarar a yankin Tadhawan dake arewacin kasar, sai dai babu bayani akan asarar rayuka.

A kasar Aljeriya ma an sami tashin gobara har a wurare 159,an kuwa yi nasarar kashe 141.

A can Amurka kuwa an sami rasuwar masu aikin kashe gobara 4 da suke kokarin kashe wutar da tashi a tsakanin jahohin Carrolina da kuma Utah. A kasar China kuwa guguwa ce mai karfi da ruwa kama da bakin kwarya suka barke a yankin Hong-kong.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted