IRGC: Babban Bala’i Ne Zai Fada Wa “Isra’ila” Idan Yaki Ya Sake Barkewa

Babban Bala'i Ne Zai Fada Wa "Isra'ila" Idan Yaki Ya Sake Barkewa
dakarun kare juyin musulunci na Iran

Kakakin dakarun kare juyin juya halin musulunci ( IRGC) Hussain Muhibbi ya bayyana cewa; Dakarunmu suna da tsare-tsare mabanbanta domin fuskantar sake barkewar yaki, za kuwa mu jefa “Isra’ila” cikin babban bala’i.

Haka nan kuma kakakin IRGC din ya ce, duk wata kasa wacce za ta taimakawa Amurka Birtaniya ce, ko kasashen wannan yankin, za su zama halartattun da za a kai wa hari.

Kakakin dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; A bayan nan Birtaniya ta bai wa Amurka damar yin amfani da filayen jiragen Samanta, to ya kamata ta kwana da sanin cewa idan ta ci gaba, to kuwa za ta zama halartaccen wacce za akai wa bara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted