Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya dawo Tehran a safiyar yau Lahadi, bayan taron kungiyar kasashen ‘ Shanghai Cooperation Organization (SCO), a birnin Cholpon-Ata, Kyrgyzstan daga ranar Alhamis 23 ga watan Juli shekara ta, 2026 da ta gabata.
Kamfanin dillancin Labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan a jawabin da ya gabata a taron ya kara bayyana muhimmancin aiki tare tsakanin kasashen kungiyar saboda hana Amurka kara fadada halayenta na nuna karfi a kasashen yankin.
Labarin ya kara da cewa ministan ya gana da tokwarorinsa guda 6 a gefen taron, kuma sun hada da Rasha, China, Uzbekistan, Belerus, Pakistan da kuma mai masaukin baki Kyrgizstan.
A taron dai kasashen kungiyar ta ‘ Shanghai Cooperation Organization (SCO), sun amince da abubuwa guda 9, sannan sun rattaba hannu kan yejeniyoyi 25 da kasar Iran.
Aragchi ya bayyana muhimmancin wannan taron musamman a dai dai lokacin kasarsa take fafatawa da Amurka wacce take nuna karfi da babakera a cikin al-amuranta a doron kasa.