An Gudanar Da Zama Tsakanin Iran Da Oman Kan Mashigar Hormuz

An gudanar da tattaunawa ta fannin fasaha tsakanin Iran da Masarautar Oman game da Mashigar Hormuz Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya sanar

An gudanar da tattaunawa ta fannin fasaha tsakanin Iran da Masarautar Oman game da Mashigar Hormuz

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya sanar da cewa: Tattaunawar da aka gudanar a birnin Tehran tsakanin Iran da Masarautar Oman game da Mashigar Hormuz ta kasance mai amfani da kuma samar da sakamako mai kyau.

Dangane da tambayoyin da ‘yan jarida suka yi game da tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da Masarautar Oman kan Mashigar Ruwa ta Hormuz, Baqa’i ya bayyana cewa: An gudanar da zagaye da dama na tattaunawa a Tehran a ranakun Juma’a da Asabar tsakanin kasashen biyu, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje. A yayin wadannan tarurruka, bangarorin biyu sun tattauna kan ka’idoji na bai-daya da kuma hanyoyin gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci ta cikin Mashigar Hormuz, tare da mutunta ‘yancin ikon mallakar kasa na kasashen biyu da ke makwabtaka da wannan mashiga.

Da yake amsa tambaya dangane da halin da ake ciki a mashigar Hormuz, Baqa’i ya bayyana cewa, ba a samu wani sauyi a matsayin mashigar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted