Shugaban Kasar Rasha Ya Ayyana Sharuddan Kawo Karshen Yakin Ukiraniya

A daidai lokacin da ake kara samun sabani a tsakanin kasashen turai dangane da yakin Ukiraniya, fira ministan kasar Hangaria ya ziyarci birnin Moscow,

 A daidai lokacin da ake kara samun sabani a tsakanin kasashen turai dangane da yakin Ukiraniya, fira ministan kasar Hangaria ya ziyarci birnin Moscow, inda ya gana da shugabanta Vladimir Putin.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya ce , ya yi ganawa take da keke da shugaban na kasar Hangaria Victor Orban, inda ya bijiro masa da sharuddan kawo karshen yakin Ukiraniya.

Putin ya ce daga cikin sharuddan da akwai janyewar dukkanin sojojin Ukirani daga jamhuriyoyin Donsik da Lgansk, sai kuma yankuna Zabarojiya da Khirson.

Tun a baya shugaban kasar ta Rasha Vladmir Putin ya jaddada cewa, kasarsa tana kallon zancen Donal Trump na Amurka na batun kawo karshen yaki da cewa yana da muhimmanci, kuma idan aka sake zabarsa a matsayin shugaban kasar Amruka, to zai kawo karshen sabanin dake tsakanin Kiv da Moscow.

A gefe daya, shugaban kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, Jane Stoltenberg  ya ce  shugaban kasar ta Hangaria ba ya waklltar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato a ziyarar da ya kai zuwa Moscow.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments