Kafar watsa labaru ta “Afircanews” ta bayyana cewa, babu wani cikakken dalili da aka gabatar dangane da sauye-sauyen, tare da kuma kore jita-jitar da aka rika watsawa akan yunkurin juyin Mulki a kasar a watan Satumba, dda ya kai ga tsare sojoji 20 daga ciki har da Birgediya janar da kuma kanar.
Mai Magana da yawun shugaban kasar ta Nigeria, ya bayyana cewa; shugaba Ahamd Tinubu ya salami manyan jami’an sojoji da su ka hada babban hafsan hafsoshi Emmanuel Ogalla, shugaban sojan ruwa, da Hassan Abubakar, shugaban sojan sama.
Shugaba Ahmad Tinubu ya nada Olufemi Oluyedi, tsohon hafsan hafsoshin soja a matsayin sabon ministan tsaro.
Sabon shugaban sojan kasa shi ne Manjo janar W. Shaibu
Shugaban sojan Sama kuma shi ne S.K Akene
Sabon shugaban sojan ruwa kuwa shi ne Rear Admiral I. Abbas
Tare da cewa babbar shalkwatar sojojin kasar ta Nigeria a Abuja, ta kore jita-jitar juyin Mulki sai dai haka bai kawar da tsoro a tsakanin ‘yan kasa ba.
Wani dan majalisar dattijai Sanata Irogebu ya ce da alama hukuma tana Fifita bai wa kanta kariya ne, fiye da sauran barazanar tsaro da ake fuskanta.