Shugaban kasar Lebanon Josepth Aoun ya yi alkawalin adalci ga iyalan wadanda fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut ya shafa bayan shekaru 5 da aukuwar hakan.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau litinin. Ya ce har yanzun ba wanda aka kama ko ake tuhuma da haddasa wannan fashewar tun aukuwarsa a ranar 4 ga watan Augustan shekara 2020.
Labarin ya kara da cewa Fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut shi ne fashewa mafi muni bayan na manyan manyan makamai kare dangi, inda a wannan karon taki wanda aka yi shi da sinadarin ‘Amonium nitrate’ ya fashe ya kuma kashe mutane 220 sannan wasu kimani 6,500 suka ji rauni da kuma asarar dukiyoyin wanda ya kai biliyoyin dalar Amurka.
Shugaba Aoun ya cewa sai gudanar da bincike tun asalinsa, don gano yadda aka ajiye takin a inda aka ajiye shi da kuma musabbabin fashewarsa. Ya ce ba wanda za’a bari idan har bincike ya kai kansa.