Shugaban Kasar Iran Yana Son Ganin Duniya Ta Dauki Matakin ‘Yantar Da Al’ummar Falasdinu

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna son duniya ta daukin matakin ganin an ‘yantar da al’ummar Falasdinu daga mamaya da kuma kashe-kashen gilla Shugaban

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna son duniya ta daukin matakin ganin an ‘yantar da al’ummar Falasdinu daga mamaya da kuma kashe-kashen gilla

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Wasu masu da’awar kare hakkin bil’adama suna gudanar da mu’amala kan batun hakkin Falasdinawa a kan tubalin nuna wariyar launi da jinsi, yana mai fayyace cewa: Wadanda suke goyon bayan masu kisan yara a Gaza, ba zasu taba wanzar da zaman lafiya ba, yana mai jaddada cewa; Iran na son ganin duniya ta dauki matakan ‘yantar da al’ummar Falastinu daga mamaya da kuma kashe-kashen gilla.

A cikin jawabin da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gabatar a wajen bikin rantsar da shi ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai iya aiki a matakan hadin gwiwar kasa da kasa da al’adu da kiyaye mutunci da hakkokin mutane.

Ya yi nuni da cewa, zabukan da aka gudanar a baya-bayan nan sun nuna cewa al’ummar Iran suna neman cimma manufofi da dama ta hanyar rayuwa da zaman lafiya, don haka dole ne su damu da al’ummar Iran a matsayin damammaki da kuma yin aiki don ci gabansu.

Shugaban ya kara da cewa: Suna da damar karfafa alaka da kasashe ba tare da yin kasa a gwiwa ba, saboda Iran kasa ce mai aminci da kwanciyar hankali, kuma zaben da aka gudanar a cikin kasar ya tabbatar da haka musamman yadda aka gudanar da zabe cikin aminci da inganci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments