Shugaban Kasar Iran Ya Nada Muhammad Reza Arifi A Matsayin Mataimakin shugaban kasa Na Daya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya nada Muhammad Reza Arifi a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko. Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya nada Muhammad Reza Arifi a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto majiyar ofishin shugaban kasar ta na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin wani umurnin da shugaban ya rubuta, ya bayyana cewa, ya zabi Arifi a matsayin mataimakin shugaban kasa ne, saboda gogewarsa da kuma dadewar da yayi yana ayyukan shugabanci a ma’aikatu gwamnati daban daban a kasar.

Ya kuma bukaci mataimakin shugaban kasar na farko yayi matukar iyawarsa don tabbatar da harkokin ci gaban kasa suna tafiya kamar yadda aka tsara tafiyarsu.

A bisa doka ta 124 na kundin tsarin mulkin JMI dai shugaban kasa na iya zamar duk wanda yaga ya dace ya zama mataimakinsa na farko.

Reza Arifi dai yana daga cikin jami’an gwamnati na 14 na farko farko wadanda shugaban ya nada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments