Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Amurka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta zurfafa zuba jarin Amurka a fannin haƙar ma’adinai tare da inganta sarrafa albarkatun ma’adinan kasar. Ministan Ma’adinai na kasa, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin New York.
Alake ya bayyana cewa yarjejeniyar ta kunshi tattara bayanan kasa da binciken ma’adinai, bunkasawa da sarrafa ma’adinan, samar da ababen more rayuwa da kuma ƙara ƙwarewar ma’aikata.
Ministan ya ce Najeriya ba za ta ci gaba da kasancewa kasar da ake kwashe albarkatun kasa ba tare da samun cikakkiyar ribar da suke samarwa ba, yana mai cewa gwamnati na son kara sarrafa ma’adinai a cikin gida, samar da ayyukan yi da bunkasa kwarewar ‘yan Najeriya da harkokin kasuwancinsu.
Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tarayya ke kara kokarin jawo jarin kasashen waje zuwa bangaren ma’adinai tare da kara darajar albarkatun da ake sarrafawa a cikin Najeriya.