Babban Muftin Saudiya Ya Bukaci Sojoji Su Kai Hari Kan Yamen

wani babban malami a kasar saudiya ya bukaci dakarun sojin kasar da su kai hare hare kan kasar yamen

Rahotanni sun nuna cewa babban muftin kasar saudiya yayi kira ga gwamnatin kasar saudiya da dakarun hadin guiwa da su sadaukar da rayukansu wajen kai hare-hare kan kasar yamen a daidai lokacin da kasar faransa ta ce za ta aike da dakarun soji da kayayyakin tsaro  zuwa saudiya adaidai lokacin da saudiya ke fuskantar mummunan harin mayar da martani daga dakarun kasar Yamen

 Yankin Yanbu yana dauke da manyan wurare na ajiye man fetur da aka tace, kuma yana da alaka da bututun mai na gabas zuwa yamma, wanda ke da damar jigilar danyen mai har zuwa ganga miliyan 7 a kowacce rana

Biyo bayan hare haren da amurka da isra’ila suka kai wa iran da kuma matakin da rundunar sojin iran ta dauka na rufe mashigar Hurmuz ga jiragen ruwan amurka da na kawayenta, kasar saudiya ta dogara ne kan bututun mai na gabas zuwa yamma wajen fitar da manfetur dinta zuwa kasashen waje.

Ana sa bangaren kakakin sojin kasar Yamen birgedier janar yahya saree ya sanar a jiya alhamis cewa dakarun sojin kasar yamen sun kai hari kan muhimman wurare a kamfanin Aramco dake Yanbu, da kuma wasu wuraren dake birnin riyad

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted