Rahotanni sun bayyana cewa sama da masu zanga-zanga 100 ne da jami’an yan sanda birnin newyork suka kama a lokacin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewasu da halartar taron majalisar dinkin duniya da fira ministan isra’ila banyamen na tanyaho yayi,
A jiya alhamis ne a ka yi kamen adaidai lokacin da fira ministan isra’ila ke yin jawabi a babban taron majalisar dinkin duniya, inda dararuwan wakilan kasashe suka fice daga zauren a lokacin da ya fara bayani don nuna adawarsu da kasancewarsa a wajen,
Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken cewa a bari alummar gaza su rayu, dukkan duniya suna gani natanyaho bai boye wa kowa ba,ana zarginsa da yin kisan kare dangi
Ana sa bangaren mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran kan sharia da harkokin kasa da kasa kazem garib abadi ya wallafa a shafinsa na x a yau jumaa cewa fira ministan isra’ila yazo taron majalisar dinkin duniya ne domin kare wuce gona da iri da yaki da gwamnatin sahyuniya ta yi