Wasu Sojojin Isra’ila Guda 2 Sun Halaka A Arewacin Gaza

wasu sojojin isra'ila sun halaka sakamakon fashewar wani jirgin sama mara matuki a arewcin gaza

Rahotanni sun nuna cewa sojojin isra’ila guda 2 sun halaka a jiya alhamis alokacin da suke duba wani jirgin sama mara matuki da bai fashe ba a kusa da barikin soji, a arewacin Gaza, sai dai an kai su asibiti kafin daga bisani suka mutu, sai dai ana gudanar da bincike kan musabbabin afkuwar hakan,

Har ila yau kimanin sojojin isra’ila guda 5 ne aka kashe  tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta  a watan oktoba bayan kwashe shekaru 2 isra’ila na kisan gilla kan alummar Gaza

hukumar kula da kanan yara ta majalisar dinkin duniya unicef ta fitar da rahoto a farkon wannan watan cewa hare haren da israila ta kai ya lalata kayyayakin agaji da ya kai na dala 770,000 da aka kai su don tallafama yara kanana 45000 da mata masu ciki da kuma iyayaye da suke shayarwa.

Isra’ila ta kaddamar da mumunan yaki kan alummar gaza ne a ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 tare da goyon bayan Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted