Iran Za Ta Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Kara Kai Mata Hari

shugaban kasar iran yace iran za ta mayar da martani mai karfin gaske idan amurka ta sake kai mata hari
shugaban kasar Iran

Shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan yayi gargadin cewa Tehran za ta mayar da martani mai karfi idan kasar Amurka ta ci gaba da kaddamar da yaki kanta , iran bata zabi yaki ba kuma ba shi ne abin da take nema ba,

Yace bamu taba fara yaki ba amma idan ta zabi ci gaba da yaki da mu to zamu mayar da martani mai karfi da ban mamaki kamar yadda shugaban kasar iran ya bayyana a hira da fox new suka yi da shi.

Wadanan bayanan suna zuwa ne bayan dakatar da bude wuta na wucin gaji bayan kwashe kwanaki 40, bayan mayar da martani da kasar Iran tayi, Tehran da Washington sun sanya hannu na yarjejeniyar Islamabad a ranar 17 ga watan yuni, ta kawo karshen yaki. daga karshe amurka ta karya yarjejeniyar ya kai ta ta rushe,

Da aka tambayeshi game da tattaunawa ba ta kai tsaye ba tsakanin jami’an diflomasiyar iran da kuma wakilan musamman na Amurka steve witkoff da jares Kushner a birnin new York, pezeshikiyan ya bayyana cewa matsayin iran yana ci gaba da dogaro ne kan dokokin kasa da kasa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted