Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Alkawalin Adallaci A Rabon Dukiyar Kasar

Shugaban kasar Iran Masa’ud Pezeskiyan yayi alkawarin bawa dukkanin mutanen kasar Iran damar samun arziki da ci gaba tare da adalci. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban Pezeshkian  yana fadar haka jim kadan bayanda Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khamina’e ya mika masa shaidan tabbatar da shi a […]

Jagoran Juyin Musulunci ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban Iran na 9

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin sabon shugaban kasar Iran. A wani bikin da aka gudanar kuma aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar a yau Lahadi, Ayatullah Khamenei ya amince da Pezeshkian a matsayin shugaban kasar a hukumance, wanda ya  yi nasara […]

Manufar Netanyahu na rusa Hamas ba abu ne mai yiwuwa ba; Lavrov

Har yanzu Moscow ba ta ga wani mataki na gaske da zai kawo karshen zubar da jini a yankin Gabas ta Tsakiya ba, in ji ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a karshen ziyararsa a Malaysia. Lavrov ya ce “Babu wani mataki wanda aka dauka da zai kawo karshen wannan zubar da jini har yanzu. […]

Bagheri Kani: Matakin siyasa na rufe cibiyar Musulunci a Jamus hidima ce ga Isra’ila

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Iran Ali Bagheri Kani ya ce matakin “siyasa” da Jamus ta dauka na rufe Cibiyar Musulunci ta Hamburg (IZH) da rassanta da nufin biyan muradun gwamnatin Isra’ila. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a ranar Asabar, Bagheri Kani ya yi kakkausar suka ga matakin […]

Isra’ila Ta Sake Kashe Wani Adadi Mai Yawa Na Mata Da Kananan Yara  A Gaza

Sojojin Isra’ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa 41 a hare-hare da suka kai a Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a yankin ya kai 39,258 tun daga 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta yankin. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ƙara da cewa mutum aƙalla 90,589 ne […]

Iran da China sun tattauna batun inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa, gwamnatocin kasashen Iran da China sun kudiri aniyar kara inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Wannan bayanin ya biyo bayan ganawarsa da jakadan kasar Sin a Tehran Zong Peiwu, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ayyukan […]

Hezbollah: ‘Isra’ila’ ce ke da hannu a harin Golan

Gwamnatin Biden ta bayyana damuwarta kan harin da aka kai jiya Asabar kan tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye, wanda Amurka ke zargin cewa “daga Labanon ne”, wanda a cewar Amurka zai iya kara tsananta yaki tsakanin Hizbullah da Isra’ila, a cewar rahoton Axios. Zargin na Amurka dai na zuwa ne duk da […]

Rahoto: Babu Sauran Wata Mafaka Ga Fararen Hula A Cikin Zirin Gaza

Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan da Isra’ila ta kwashe makonni tana kai musu hari babu inda za su je, ɗaruruwan Falasdinawa sun koma ɓuya a wani tsohon gidan yarin Gaza da aka gina domin tsare masu laifin kisan kai da ɓarayi. Yasmeen al-Dardasi ta ce ita da ‘yan’uwanta suna ji suna gani suka dinga […]