A yau Talata ne dai shugaban “Isra’ila” Isaac Herzog ya isa birnin Addis Ababa da zai yi dauki kwanaki biyu yana Ziyara.
A filin saukar jiragen saman a babban birnin kasar ya sami tarbar ministan harkokin wajen, ana kuma sa ran cewa zai gana da shugaban kasar Salassie da fira minista Abiy Ahmad.
Wannan ziyarar a Afirka tana zuwa ne, bayan kwatankwacinta da shugaban haramtacciyar kasar ta yahudawa ya kai zuwa yankin Somaliland da ya jawo cece-kuce.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da daukar yankin na Somaliland da wani yanki ne na kasar Somaliya da cewa, kasa ce mai cin gashin kanta. ‘Yan sahayoniyar dai suna kokarin yin kutse a cikin nahiyar Afirka da samun tasiri.
Gaganin ziyarar shugaban haramtacciyar kasar ta yahudwa, Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya ziyarci Addis Ababa da a can ya yi kira kar a bar yankin ya zama wajen fadace-fadace na kasashen waje.