Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Tsaron ‘yan ƙasa jan layi ne, kuma ba za su janye daga taruwa a sha tale-tale ko tattaunawa ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Gwamnatinsa ba za ta yi watsi da taruwan jama’a kan sha tale-talen kan hanyoyi ko kuma kauracewa teburin tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Babban abin da Iran ta fi mayar da hankali a kai shi ne kare tsaron kasa da kuma tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron ‘yan kasarta.
A wani rubutu da ya yi a dandalin sada zumunta na X a ranar Litinin, ya rubuta cewa: Abin da kasarsa ta fi mayar da hankali a kai shi ne tsaron kasa da kuma walwalar mutanenta, yana mai jaddada cewa: Iran za ta kare hakkokin ‘yan kasarta sosai kuma ba za ta ja da baya ba idan har ta fuskanci wata barazana.
Shugaban ya kammala jawabinsa da cewa: Diflomasiyya da tsaro sune ginshikai biyu na karfin kasa, yana mai nuna cewa Iran ba zata janye daga kan sha-tale-talen hanyoyi ko teburin tattaunawa ba, kuma kasar za ta yi nasarar shawo kan wannan mataki albarkacin hadin kai da hankali.