Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dole ne Amurka ta ajiye duk wani girman kai da barazanar yin amfani da karfi , yana gargadin cewa yin amfani da irin wannan mataki zai kara dagula duk wani kokari da ake yi ne na aiki da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma da kuma warware matsalolin yanki
A lokacin ganawarsa da kwamandan dakarun sojin kasar Pakistan kuma ministan tsaro field mashal Asim Munir, pezeshkiyan ya nuna gamasuwarsa game da rawar da kasar pakistan ke takawa na shiga tsakani na ganin an samu zaman lafiya da tsaro a yankin, kuma yayi fatan cewa kudurin siyasa da ake da shi da yin aiki tare zai taimaka wajen cimma buri a yarjejeniyar da aka cimma.
shugaban yace wajibi ne kasar Amurka ta girmama alkawuran da ta dauka ga kasar iran kan hakkokinta da dakoki suka bata da kuma tsari na kasa da kasa, kuma yayi ishara game da juriya da tsayin daka da alummar iran suka nuna sakamakon hadin kai da suke da shi, wanda shi ne yasa za ta iya shawo kan dukkan matsaloli da barazana da suke fuskanta
Ana sa bangaren field marshal Munir ya godewa shugaban kasar Iran game da namijin kokarin da yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma ya nuna fatansa na cewa kawo karshen wannan rikicin zai bude sabon shafi na yin aiki tare wajen sake gina yankin da bunkasashi da kuma samun cikakken tsaro.