NNPC Ya Rattaba Hannu Da Wasu Kamfanoni Kan Hako Mai

Matatar mai ta najeriya ta kulla yarjeniyoyi da kamfanoni wajen hako mai a cikin teku

Kamfanin mai na Najeriya NNPC da wasu kamfanonin mai sun kulla yarjejeniyar fadada aikin hako mai na karkashin teku a Bonga, wanda ake sa ran zai janyo zuba jarin da ya kai dala biliyan 15 zuwa 21.

Baya ga NNPC, kamfanonin da suka rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar kwangilar ta OML 118, sun hada da Kamfanin mai na Shell, da na Esso wanda ya kware a fannin hako mai a karƙashin teku, da kuma Kamfanin NAE.

Yarjejeniyoyin sun kunshi rarraba aikin kwangilar, da ta warware takaddamar aikin DSA, wanda ake sa ran zasu taimaka wajen habaka shirin hako man a Bonga dake kudu maso yammacin Najeriya zuwa matakin da masu zuba jari zasu shigo cikinsa.

Wannan ci gaba ya biyo bayan sabuwar dokar da shugaba Tinubu ya amince da ita ne, ta aikin hako mai a karƙashin teku da kuma iskar Gas, wadda ke da matukar muhimmaci a shirin gwamnatin na fadada harkar hakar mai a kasar mai arzikin ma’adinai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted