Ofishin Shugaban Kasar Iran: Ziyarar Hafsan Hafsoshin Sojan Pakistan Ta Haifar Da Da Mai Ido

Ofishin sandarwa na shugaban kasar Iran ya sanar da cewa ziyarar da Babban hafsan hafsoshin sojan Pakistan ya kawo zuwa Iran ta haifar da Da,
Ziyarar Asim Munir Zuwa Iran

Ofishin sandarwa na shugaban kasar Iran ya sanar da cewa ziyarar da Babban hafsan hafsoshin sojan Pakistan ya kawo zuwa Iran ta haifar da Da, mai ido.

Kamfanin dillancin labarun “Tasnim” ya ambato ofishin watsa labaru dake karkashin ofishin shugaban kasa yana cewa; ziyarar da Field Marshel Asim Munir na Pakistan ya kawo Iran ta sa an cimma wasu muhimman manufofi na diplomasiyya.

Shugaban ofishin watsa labaru Taba’tabai ya ce; Sabanin hasashen da ake yi  a cikin kafafen watsa labaru da ba su da tabbaci, an cimma manufofin da ba da jimawa ba za a ga sakamakonsu a kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted