Babban magatakardar MDD Antonio Guterres wanda yake Ishara da yakin da Amurka ta kallafa wa Iran ya bayyana cewa; Wajibi ne ga kasashe da su fahimci cewa karfi yana da iyaka.
Haka nan kuma babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce; Abubuwan da su ka faru a cikin shekarun bayan nan, suna nuni da cewa, yadda manyan kasashe su ka yi kokarin damfarawa wasu kasashe manufofinsu yana da iyaka.
Jaridar “Financial Times” da ake bugawa da Birtaniya ta dauki jawabin da babban magatakardar MDD yana yin Ishara da tsaka mai wuyar da Amurka ta shiga a yaki da Iran da kuma yakin Ukiraniya da suke a matsayin kwakkwaran dalili na abinda karfin soja zai iya yi.
Jaridar ta bayyana cewa; A farkon yaki, abinda Amurka ta tsammaci zai faru, shi ne Tehran ta mika wuya,to amma bayan gushewar watanni shida daga fara yakin, Amurka ta kasa cimma manufar da ta bayyana.
Bugu da kari babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi bitar sauye-sauyen da aka samu a fagen siyasar duniya,don haka ya zama wajibi ga manyan kasashe da su yi aiki da abinda yake faruwa a kasa.
Da kuma ya tabo batun raguwar karfin tasirin Amurka a duniya, Guterres ya ce a halin yanzu duniya tana kan hanyar zama mai cike da manyan kasashe mabanbanta,don haka matukar ba a yi wa cibiyoyin kasa da kasa gyara da kwaskwarima ba, to abinda zai faru anan gaba shi ne fada a tsakanin manyan kasashen.