Amurka Ta Sanar Da Sabin Takunkumin Ta’addanci Kan Kasar Iran

Amurka ta sanyawa iran takunkumin taaddanci a don karya tattalin arziki

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka ta bayyana sabon haramtaccen takunkumin da ta kakaba ma kasar Iran karkashin abin da ta kir da opretion economic outrage wanda ke barazanar hukumta duk wata kasa ko wata kungiya da ke da alaka da iran, a wani yunkuri bayan  kasa cimma burinta ta hanyar matsin lambar tattalin arziki da kuma hare-haren soji kan kasar iran

Sakataren baitil malin Amurka Scott bessent ya sanar a jiya litinin cewa sabon takunkumin ta’addancin yayi dai dai da  na lokacin yakin duniya na biyu, kuma yayi ikirarin cewa mataken sun shafi hada-hadar kudi na iran da duk duniya kuma tayi gargadin cewa babu wani abokin hulda da ya fi karfin Amurka

wannan sanarwar ta zo ne adaidai lokacin da amurka ke nuna alamun rashin gamsuwa bayan kwashe watanni da dama tana kai hare-haren soji kan kasar Iran da bai yi nasara ba, da kuma kawanyar da tayi wa jiragen ruwanta don karya tattalin arzikinta

kasar china ce babbar abokiyar hulda kasar iran kuma tuni ta yi watsi da wannan mataki , ofishin jakadancin beijin a washinton ya bayyana cewa sanya takunkumi ko matsin lamba ba zai taimaka wajen warware matsalar ba,  ya yi kira da abi hanyar siyasa da diflomasiya wajen warware takaddamar da ke tsakani .

Tuni kasar Iran ta watsi da wannan haramtaccen matakin na Amurka kuma ta bayyana shi a matsayin takunkumin ta’addanci ,kuma babban lafi ne kan dan adamtaka

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted