Shugaban Iran: Al’ummar Iran Ba Zasu Taba Mika Kai Ga Barazana Ko Matsin Lamba Ba

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makiya ba za su iya tilasta wa Iran ta miƙa wuya ta hanyar barazana ko matsin lamba ba Shugaban

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makiya ba za su iya tilasta wa Iran ta miƙa wuya ta hanyar barazana ko matsin lamba ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Makiya Iran ba za su iya tilasta mata mika wuya ta hanyar barazana ko matsin lamba ba, yana mai lura da cewa: Yunƙurin da makiya suka yi a baya ya gaza, wanda hakan ya sa suka koma haifar da rashin jituwa da rarrabuwar kawuna a cikin ƙasar don cimma burinsu.

A lokacin da yake halartar wani biki na tunawa da ranar shahadar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, da iyalansa, wanda aka gudanar a birnin Tehran, Pezeshkian ya bayyana cewa: Dabarun ƙiyayya sun dogara ne kan ƙara ruruta wutar rarrabuwar kawuna a cikin gida, domin tilasta wa Iran mika wuya ta hanyar amfani da ƙarfin soja ko barazana al’amura ne da ba zasu yiwu ba a wannan zamani. Ya ambaci juriyar al’ummar yankin yayin da suke fuskantar matsin lamba daga waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted