Shugaban asbitin Ashif ana gaza wanda yake daga cikin falasdinawa 50 wadanda sojojin HKI suka saka daga gidajen yari sannan suka maidasu gaza, ya ce sojojin HKI sun azabtar da shi, da kuma sauran falasdinawa da suka kama bayan fara yakin Tufanul aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Mohammad Abu Salmiya yana fadar haka a wani taron yan jarida da ya kira a Gaza bayan sojojin yahudawan sun dawo da su Gaza. Abu Salmiya ya kara da cewa sojojin yahudawan suna amfani da duk wata hanya ta azabtarwa a cikin gidajen yarin kasar, wadanda suka hada da hana abinci, doka da kulki da sakin kare a kan wadanda suke tsare da su, da sauransu.
Abu Salmiya ya kara da cewa sojojin yahudawna sun kama Falasdinawa fararen hula fiye da 5000 a gaza bayan fara yakin, kuma a halin yanzu ba’a san makomar wasu daga cikinsu ba.
Banda haka ya ce tabbas sun kashe wasu, sannan likitocin yahudawan suna taikamawa sojojin wajen cutar da falasdinawa, daga cikin an yanke kafafuwan wasu saboda rashin kula da kiwon lafiyarsu. Sannan shi a karan kansa an karya masa yatsa sannan an yi masa doka da kulki har kansa y afara zubar da jinni.