Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Zai yi nazarin shawarar da Iran ta gabatar
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, “Nan ba da jimawa ba zai yi nazarin shirin da Iran ta gabatar.”
Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya ambato Trump yana cewa: “An yi masa bayani game da manufofin yarjejeniyar da Iran kuma za a ba shi cikakken bayani game da kalmomin da suka dace.”
Rahotannin sun nuna cewa: Kasar Iran, ta hanyar shiga tsakani na Pakistan, ta gabatar da martani ga shawarar Amurka mai maki tara, wacce ta fi mayar da hankali kan batun “kawo karshen yakin.”
Shawarar Amurka ta kunshi bukatar tsagaita wuta na watanni biyu, amma Iran ta dage kan warware dukkan batutuwan da ba a warware ba cikin kwanaki 30, tana mai jaddada “kawo karshen yakin” maimakon kawai tsawaita tsagaita wuta.
Maki 14 da Iran ta gabatar sun hada da batutuwa da dama, kamar: Garanti kan rashin wuce gona da irin soji, janye sojojin Amurka daga kusa da Iran, dage matakan killace jiragen ruwa, sakin kadarorin Iran da aka kame, biyan diyya, dage takunkumi, kawo karshen yakin a dukkan fannoni, ciki har da Lebanon, da kuma kafa sabuwar hanya ga shige da fice a mashigar tekun Hormuz.