Sharhin zai yi magane kan furucin wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya kuma jakadanta na din din din a Majalisar na yin tofin Allah tsine da yin Allah wadai da kakkausar murya kan cewa: Kasashe biyar na Larabawa sun bar masu kai harin wuce gona da iri kan Jamuhuriyar Mulunci ta Iran sun yi amfani da yankin kasashen su da sararin samaniyarsu.
Amir Saeed Irawani, jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aika da wasiku masu karfi ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da Kwamitin Tsaron Majalsar a ranar Laraba, yana nuna rashin amincewarsa da cewa kasashe biyar na Larabawa sun ba Amurka damar amfani da yankinsu da sararin samaniyarsu don kai hare-haren wuce gona da iri kan Iran.
A cikin wasikunsa, Jakadan Iran ya ce: “Ganin nauyin da kasashen duniya ke da shi na barin wasu su yi amfani da yankinsu don aikata ayyukan ta’addanci da kuma kai hare-hare kan yankin musamman wata kasa, wato Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana rashin amincewarta da wannan haramtacciyar aiki da ya saba wa doka.”
Wakilin Iran ya kara da cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira ga gwamnatocin Qatar, Kuwait, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masarautar Saudiyya da su bi ka’idojin makwabtaka nagari da kuma hana ci gaba da amfani da yankunansu kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”
Sa’id Irawani ya kuma ambaci lokutan da aka kai hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga kasashen da aka ambata a baya.
Sannan wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Wasu daga cikin makaman da aka yi amfani da su wajen kai wa Iran hari sun fito ne daga tarin makaman kasashen yankin Tekun Fasha.
Haka nan a cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, Jakadan Iran Amir Sa’id Irawani, ya yi watsi da ikirarin Bahrain, yana mai cewa: “Ragowar makaman da aka yi amfani da su wajen kai hari kan Iran, wadanda aka gano a wasu biranen da abin ya shafa, sun tabbatar da cewa wadannan makaman wani bangare ne na wasu kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha ne.”
A ranar Talata da ta gabata, jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Irawani, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Tsarin da Amurka ta dauka na hana zirga-zirgan jiragen ruwa na Iran keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne, kuma janye shi wani sharaɗi ne na sake fara wata tattaunawa.” Ya kara da cewa, “Yana ganin da zarar Amurka ta kawo karshen takunkumin jiragen ruwa, za a shiga zagaye na gaba na zaman tattaunawan birnin Islam-abad na Pakistan.”
Irawani ya kuma bayyana cewa, “Amurka ce ta fara kaddamar da yaki kan Iran, kuma idan tana son komawa teburin tattaunawa, to ta nemo mafita ta siyasa, Iran zata kasance a shirye take don hakan.”
Ya kara da cewa, “Idan Amurka tana son shiga yaki, Iran ma a shirye take don hakan.”
Da aka tambaye shi game da kwarin gwiwarsa game da yiwuwar sake fara tattaunawa, jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce, “Dole ne Iran ta ba da dama; kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan.”